Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, wanda ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, 2023, ya ce wanda ake zargin ya dade yana yin sojar gona da cewa shi jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma da ke ofishin 35PMF Dutse ne da kuma tsoratar da mutane.
“Kafin kama shi, an samu rahoton cewa wanda ake zargin ya tafi wani shagon Aliyu Bako da ke kauyen makanike sanye da kakin ‘yan sanda dauke da bindiga, kuma ya sayi kayayyakin abinci a kan bashi, ya kuma yi alkawarin biyansa da zarar an gyara masa asusun albashi.” PPRO ya bayyana.
Daga baya dan sandan na jabu ya kasa cika alkawari, wanda aka cuta ya kai kara ga hukumar ‘yan sanda.
"An kama wanda ake zargin ne a ranar Talata, 20 ga watan Yuni, 2023, da misalin karfe 1640."
DSP Shiisu ya ce an mika wadanda ake zargin zuwa SCID Jigawa domin gudanar da bincike mai zurfi.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com