Wani lauya mai suna, Ayo Sogunro ya bayyana yadda ya kwana a hannun 'yan sanda bayan wata kawarsa matar aure ta ziyarce shi a otal a Abuja.
Ayo ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 21 ga watan Yuni inda ya ce yazo Abuja ne don gudanar da wata ganawa akan hakkin dan Adam.
Ya ce ya kira wasu daga cikin abokansa ya tabbatar musu da cewa ya samu isowa.
Lauyan ya ce matar auren ce ta fara isowa dakin otal din
Daya daga cikin abokan nasa mace ce da ta fara isowa, zuwanta ke da wuya sai ga jami'an 'yan sanda sun shigo dakin da yake, Punch ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son
A cewarsa:
"A cikin mutanen da na turawa sakon na iso, ita ta fara zuwa, na shiga dakina da misalin 6:20 na yamma, ita kuma ta karaso 6:40 na yamma.
"Bayan mintuna 15 sai ga 'yan sanda a bakin kofar otal din, inda suka bukaci shiga cikin dakina.
"Na hana su shiga inda nace ba su da damar yi mini kutse, sai suka ture ni suka shige cikin dakin.
"Sai suka kira matar suka bukaci ta zo su tafi da ita, muka tambayi dalili, suka ce ai matar aure ce bai kamata ta kasance da ni a dakin otal ba."
Samuel ya yi wannan koken ne bayan da Sanata Adamu Bulkachuwa ya yi katobara a zauren majalisar dattawa.
Sanatan ya yi subut da baka inda ya ce yana da tasiri wurin hukuncin da matarsa ke yanke wa a kotu.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com