Sabon gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce babu wata mota da tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya siya kan kudi naira miliyan 2,794,337,500 bayan ya bar mulki a ranar Litinin da ta gabata.
Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai , Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana haka a wata sanarwa a ranar Asabar, 3 ga watan Yuni, inda ya ce tsohon gwamnan ya bayar da kwangilar siyan motocin da za a raba wa manyan mutane da sauran ma’aikatu, da hukumomi (MDAs). ) akan N1,149,800,000. An bayar da kwangilar siyan motocin ga Hafkhad Properties and Facilities Management Nig. LTD.
An kashe Naira 484,512,500 kan Jeep mai kariyar harsashi guda uku; N459,995,000 na nau'ikan Prado Jeep guda bakwai masu kariyar harsashi, da Land Cruiser; da N228,830,000 na Toyota Hilux guda bakwai.
An biya Naira 61,200,000 kan Seti 30 na Peugeot 406; N130,000,000 na Land Cruiser daya mai kariyar harsashi da N160,000,000.00 na mota kirar Land Cruiser Jeep guda biyu, yayin da aka siya motoci uku kan N120,000,000 ga ofishin mataimakin gwamna.
Ya kuma bayyana cewa sun bukaci Bello Matawalle da mataimakinsa da su mayar da dukkan motocin da suka bata cikin kwanaki biyar (5) ma aiki.
BY isyaku.com