Tsananin luguden wuta na Dakarun Sojoji a Borno ya sa yan ta'addan ISWAP sun nutse cikin Kogi a kokarin tserewa


Aƙalla mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan Islamic State of West African Province(ISWAP), 82 ne tare da iyalansu suka nutse a cikin wani rafi a yankin Damasak na jihar Borno. Legit ya wallafa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴan ta'addan tare da iyalan na su sun fito ne daga yankin tafkin Chadi, sun nutse ne yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa jamhuriyar Nijar, a ƙoƙarin tserewa luguden wutan da dakarun sojoji suka kwashe kwana biyu suna yi musu a tsakanin ranakun 2 da 3 na watan Yuni

Majiyoyi masu tushe sun tabbatarwa da Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, cewa lamarin ya auku ne daban-daban a tsakanin ƙauyukan Bulama Modori, Kaneram, Dogomolu da Jokka.

Rafin ya faro ne tun daga Komadougou a jihar Yobe, ya biyo ta tafkin Chadi sannan ya shige jamhuriyar Nijar.

Majiyoyin sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun yi ƙoƙarin tserewa ne bisa tsoron halaka a fagen daga bayan sun samu labarin cewa dakarun sojoji sun ƙaddamar da wani atisaye na musamman a yankin.

Mafi yawan waɗanda suka mutu mata ne da ƙananan yara waɗanda ba za su iya yin iyo ba, yayin da wasu kuma da dama suke jinyar wahalar da suka sha. A halin da ake ciki ana cigaba da tsamo wasu gawarwakin.

A wani labarin na daban kuma, dakarun sojojin rundunar haɗin guiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF), sun sheƙe ƴan ta'addan ISWAP a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun halaka ƴan ta'adda mutum uku na ISWAP, a wani sintiri da suka fita a yankin tafkin Chadi a jihar Borno.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN