Gwamnatin jihar Zamfara a ranar Talata ta ce ba za su taba shiga tattaunawar zaman lafiya ba ko kuma su shiga cikin wata tattaunawa da ‘yan bindiga a jihar. Daily trust ta rahoto.
Da yake zantawa da manema labarai a garin Gusau sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Nakwada ya ce gwamnati mai ci ba ta da niyyar shigar da duk wani shugaban ‘yan bindiga ko wakilinsu a tattauna komi, da sunan yarjejeniyar zaman lafiya.
Nakwada ya bayyana shirin gwamnatin jihar na, maimakon haka, ta bi ‘yan bindigar zuwa duk inda suke tare da murkushe su ciki har da masu daukar nauyinsu.
Ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tukuru tare da hadin gwiwar jami’an tsaro don ganin an kai ga yaki da rashin tsaro.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com