AN SAMU GOBARAR FASHEWAR GIDAN SAYAR DA ISKAR GAS A AZARE
Daga Muazu Hardawa Bauchi
Illustrative please |
An samu gobarar fashewar takwanen iskar gas a wani gidan sai da gas na girki da ke kan hanyar zuwa Misau a cikin garin Azare da ke Jihar Bauchi a safiyar wannan litinin, sai ko har zuwa yanzu ba'a san dalilin tashin gobarar ba.
Amma wani mazaunin garin da lamarin ya abku kan idon sa, Malam Kamal Ahmed ya ce babu asarar rayuwa ko rauni saiko asarar dukiya. Yace Jami'an kashe gobara da jami'an tsaro sun halarci wurin ba tare da bata lokaci ba don kai dauki kuma an yi nasarar kashe wutar.
Mamallakin wurin mai suna Alhaji Kawu tun farko ya jima da bude wannan wajen sayar da iskar gas a kusa da tashar Mota ta hanyar zuwa Misau.
Amma ganin irin hatsarin da ke tattare da wannan sana'a sai gwamnati ta fitar da shi daga inda yake zuwa wajen gari kuma ya kawatar da wajen bisa yadda doka ke so, ya ci gaba da harkar har lokacin da wannan tsautsayi ya abku a wajen.
Dukkan kokarin da muka yi don jin ta bakin mamallakin wurin da hukumomin tsaro ya ci tura sai ko nan gaba idan mun ji ta bakin su za mu sanar da masu karatu.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com