Shugaba Tinubu ya kori Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Tarayya



Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya amince a ruguza daukacin shugabannin majalisun da ke kula da ayyukan ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Tashar talabijin ta kasa ta ce umarnin shugaban kasar ya shafi ma’aikatu, cibiyoyi, hukumomi da uk wani kamfanin gwamnatin tarayya da ke Najeriya. Legit ya wallafa.

Hakan ya na zuwa ne jim kadan bayan Bola Tinubu ya kora hafsoshin tsaro da kwastam

.Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, jawabin ya fito a ranar Litinin ta bakin Willie Bassey wanda shi ne Darektan yada labarai na sakataren gwamnati.

Akwai wadanda abin bai shafa ba?
Ruguje shugabannin da aka yi bai shafin wasu ma’aikatu da hukumomin da ba su cikin karkashin sashe na 153 (i) na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ba.

Sanarwar ta shaida cewa wadanda abin ya shafa za su tattara su bar ofis ba tare da bata lokaci ba. Punch ta ce irinsu INEC, FCC, CCB, RMFAC da PSC sun tsira.

Idan ana neman sa hannu fa?
Idan akwai bukatar wani aikin da ya shafi sa hannun majalisun sa-idon da aka rusa, sanarwar ta umarci hukumomin su kai maganar zuwa ma’aikatunsu.

Wadanda su ke a matsayin Minitoci a yau za su dauki mataki a madadin majalisar. Hukumomin nan za su aika takardunsu ta karkashin manyan Sakatarori.

Su kuma Sakatarori za su gabatar da bukatun hukumomi, cibiyoyi, ma’aikatu ko kamfanonin zuwa ga shugaban kasa ta ofishin sakataren gwamnatin kasa

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN