Tashin hankali: Jirgin sama ya zame daga titinsa dauke da fasinjoji


A ranar Larabar da ta gabata ne wani jirgin sama na kamfanin jiragen sama na United Nigeria Airlines ya tsallake rijiya da baya a bangaren filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

 An shiga firgici a tsakanin fasinjoji 50 da suka hau jirgin da ya taso daga Ebonyi. PM News ta rahoto.

 Shugaban Kamfanin Sadarwa na Kamfanin Achilleus-Chud Uchegbu, ya ce jirgin ya sauka lafiya amma an tilasta masa dakatar da zirga-zirga zuwa gefen titin jirgin.

 A cewarsa, dukkan fasinjojin sun sauka lafiya kuma an dauke su zuwa dakin isowa tare da jakunansu.

 Ya ce jami’an hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) suna wurin da lamarin ya faru.

 Ya ce FAAN, tare da injiniyoyin UNA suna aiki don kwashe jirgin zuwa hangar.

 Uchegbu ya kara da cewa an sanar da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya NCAA da Hukumar Binciken Hatsari (AIB) yadda ya kamata kuma suna wurin.

 Ya ce kamfanin jiragen sama na United Nigeria Airlines na ba da cikakken hadin kai ga hukuma.

 Uchegbu ya ce, kamfanin ya saba kiyaye ka'idojin aminci a cikin ayyukansa kuma zai ci gaba da ba da fifiko ga lafiyar fasinjoji a kowane lokaci.

 A ranar 7 ga Mayu, 2023, jirgin Max Air ya yi hatsari a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe tare da fasinjoji 143 da wani jariri da suka tsira da ransu. 

 Tayoyi biyu na jirgin sun kama da wuta bayan ya yi saukar gaggawa inda ya tarar da jami'ai da ke kashe gobara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN