Wani asibiti ya kwace gawar Jeremiah ‘Jerry’ Okorodudu, wanda ya ci lambar zinare a gasar wasannin motsa jiki ta Oluyole 1979 a Ibadan.
Asibitin ya kwace gawar ne saboda wasu makudan kudi naira 600,000 na magani da ba a biya ba. PM News ya rahoto.
Matar Okorodudu, Adenike, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.
"Ya rasu a yanzu amma har yanzu muna bukatar biyan N600,000 domin fitar da gawarsa daga asibiti," Adenike ta shaidawa jaridar The PUNCH.
Jerry ya mutu ranar Laraba yana da shekaru 64.
Ya wakilci Najeriya a gasar Olympics ta Los Angeles 1984, inda ya fafata a matakin matsakaicin nauyi.
Ya ci lambar zinare a gasar wasannin motsa jiki ta Oluyole 1979 a Ibadan.
Matsalar lafiyarsa ta fara ne a cikin 2020 indaya yi fama da ciwon kaluluwar matsi-matsi wanda ya shafi motsinsa. Daga nan aka yi nasarar yi masa tiyata a asibitin Dans da ke Ikorodu a Legas.
Amma yanayin lafiyarsa ya sake komawa bayan da aka gano cewa yana da ciwon kafa kuma ya sami bugun zuciya.
Published by isyaku.com