Nadin mukamai: Tinubu zai iya watsi da tsoffin Gwamnoni ya nada kwararru, duba dalili

Shugaba Tinubu

A lokacin da ‘yan siyasa su ke kara huro wuta domin samun kujerar Minista, ana tunanin Bola Ahmed Tinubu ya na da ra’ayi na dabam.

Rahoton da aka samu daga Vanguard ya shaida cewa Bola Ahmed Tinubu bai so ya cika kujerun Ministoci da tulin tsofaffin gwamnoni ‘yan siyasa. Legit ya wallafa.

Wata majiya ta ce shugaban kasar ya fi sha’awar ya yi aiki da kwararru a ma’aikatun tarayya. A Kudu kuma ya samu sabani da wasu gwamnoni.

Hakan ya jawo ake tunani Bola Tinubu ba zai ba wasu daga cikin Gwamnonin da su ka sauka daga mulki a Mayu mukami a majalisar zartarwa ba.

Mecece mafitar tsofaffin Gwamnoni?

A halin yanzu akwai tsofaffin Gwamnoni daga jam’iyyun APC mai mulki da PDP mai adawa da su ke kamun kafar samun Minista ko wata kujerar.

Baya ga Ministoci akalla 36 da za a nada, akwai mukamai a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya bayan an ruguza majalisunsu.

Jaridar ta ce akwai tsofaffin Gwamnoni musamman daga jihohin Arewacin Najeriya da ke harin mukamai, amma shugaban kasar yana ta guje masu.

Wani na kusa da fadar shugaban kasa ya nuna cewa ‘yan siyasan su na so su kawo wadanda za a ba mukamai, sannan su tsira da matsayin Ministoci.

An ci moriyar ganga?

Halin da ake ciki a jam’iyyar APC shi ne wasu da suka yi mulki a jihohin Arewa sun zama karfen kafa ga Bola Tinubu ganin tasirinsu ya ragu a siyasa.

Duk da sun gagara taimakawa APC mai-ci wajen samun nasara a jihohinsu da su ke kan mulki, tsofaffin Gwamnonin su na ganin sun taimaki Tinubu.

Akwai wadanda sun karbi kudin kamfe wajen Shugaba Tinubu a lokacin zabe, sannan majiyar ta ce yanzu su na neman kwangiloli a Aso Rock.

"Omo Agege ya ci amana"

Wasu jagororin jam’iyyar APC a Delta sun rubutawa Bola Tinubu wasika a kan Ovie Omo Agege, an ji labari su na zarginsa da lafin yakar Shugaban kasar.

‘Yan siyasar sun fallasa yadda tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kawo Godwin Emefiele domin hana Bola Tinubu nasara a zaben gwani.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN