An yanke wa wani matashi dan shekara 23, Jackson Manamela, hukuncin daurin rai da rai kan wata tsohuwa mai shekaru 84 a birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu.
Kotun yankin Mahwelereng da ke Pretoria ta yanke wa Manamela hukunci a ranar Talata, 21 ga watan Yuni, 2023, bayan ta same shi da laifin fashi da makami da fyade.
Lokacin da lamarin ya faru a watan Mayun 2022, Manamela na kan beli bayan an kama shi da laifin fasa gida da niyyar yin sata da kuma yin fashi a gidan tsohuwar.
Kotu ta ji cewa Manamela ya sami matar mai shekaru 84 da haihuwa tana dafa abinci a wajen rumfar ta a ranar 9 ga Mayu, 2022 a kauyen Millennium da ke karkashin gundumar Mahwelereng da ke wajen Mokopane," Kakakin 'yan sandan Limpopo, Kanar Malesela Ledwaba ya bayyana.
"Ba zato ba tsammani ya kai hari tare da daba wa tsohuwar almakashi a goshi sannan ya jawo ta cikin rumfar," in ji Ledwaba.
Manamela ya yi wa matar fashin kudi R70 da kuma katin bayar da tallafi na jama’a. Ya ci gaba da yiwa tsohuwa fyade kafin ya gudu daga wurin.
“Bayan haka, tsohuwar ta je gidan makwabcinta ta sanar da su halin da ake ciki, nan take aka gayyaci ‘yan sanda zuwa wurin.
"Nan da nan aka bude shari'o'in fashi da makami, sannan aka kama wanda ake zargin bayan kwanaki uku kacal a ranar 12 ga Mayu, 2022," in ji Ledwaba.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com