Yin waya fiye da minti 30 a sati na kara hawan jini —Bincike


Masana kiwon lafiya sun gano cewa yin waya na sama da minti 30 a mako guda na haddasa karuwar cutar hawan jini da kashi 12. Daily trust ta wallafa.

Rahoton da Kungiyar Likitocin Zuciya na Nahiyar Turai ta fitar a ranar Juma’a ya bukaci jama’a da su takaita yin waya domin kare lafiyar zukatansu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa rahoton likitocin da aka wallafa a mujallar Digital Health yana nuna yin waya na sama da minti 30 a mako na kara barazanar kamuwa da cutar hawan jina da kashi 12 cikin 100.

Mujallar, wadda a mayar da hankali a kan yadda na’urorin zamani ke shafar lafiyar zuciya, ta ce hakan bai shafi yawan shekarun da mutun ya yi yana amfani da waya ko sanya waya a lasifika ba.

Farfesa Xianhui Qin na Jami’ar Aikin Likita tat Kudancin Guangzhou da ke kasa China, ya kara da cewa masu amfani da waya sun fi mara sa yi yiwuwar kamuwa da hawan jini da kashi 7 cikin 100.

Farfesa Qin ya a halin yanzu kusan biliyan 1.3 masu shekaru 30 zuwa 70 na da hawan jini, wadda ke iya kawo shanyewar barin jiki da kuma mutuwa farat-daya.

Masanin ya bayana cewa “Wayoyin hannu na fitar da maganadisun da ke kara hadarin kamuwa da hawan jini bayan wani lokaci.

“Duk da haka yanayin amfani da waya da ke kawo hawan jini ya bambanta a tsakanin masu kira ko amsawa, da kuma masu tura sakonni ko kuma yin wasanni da ita,” in ji Farfesa Qin.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN