Siyasar Dattaku: Sanatocin Arewa 2 Sun Janye Daga Takarar Shugaban Majalisar Dattawa, Sun Koma Bayan Wani


Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Sanata Ali Ndume, da Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano, sun janye daga takarar kujerar shugaban majalisar dattawa.

Jiga-Jigan sanatocin jam'iyya mai mulki watau APC sun hakura da takara ne jim kaɗan bayan gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya janye kuma ya marawa Godwill Akpabio baya.

A wani taro da ya gudana a gidan gwamnan Ebonyi da ke Abuja, Umahi ya ce ya hakura da takara, kuma ya koma bayan wanda APC ta zaɓa a matsayin ɗan takarar maslaha, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Tinubu da APC sun amince Akpabio ya zama shugaban majalisar Dattawa, Barau Jibrin kuma mataimakinsa.

Ndume da Barau sun bi sahun Umahi
Da yake tabbatar da janyewarsa, Sanata Ndume ya ce zai jagorancin yaƙin neman zaben Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10 da za'a rantsar a watan Yuni.

Tribune ta rahoto Ndume na cewa:

"Ba janye wa daga takara kaɗai na yi ba, ni zan jagorancin yakin neman zaben Akpabio saboda shi zababben shugaban ƙasa ya marawa baya kuma mun ji mun miƙa wuya domin kishin jam'iyya."

"Asiwaju ya ce ni ya kamata na jagoranci kamfen Akpabio, kun ga yanda ya yi kaurin suna. Saboda haka muna bayan tikitin Akpabio da Barau."

Akpabio ya maida martani
Da yake martani, Akpabio ya ƙara gode wa takwarorinsa bisa goyon bayan burinsa na zama shugaban majalisar dattawa.

Ya ce:

"Na miƙa komai ga Allah kuma a koda yaushe na kance In Sha Allah, idan Allah ya so abinda ya tsara ne zai faru a Najeriya."

Hukumar sojin ta ce ta shirya tsaf zata muƙushe duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN