Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi dan shekara 22 mai suna Ibrahim Musa, wanda ya kashe mahaifiyarsa da wuka a karamar hukumar Nassarawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, 5 ga watan Mayu, 2023, ya ce an kama wanda ake zargin ne a wata maboyar miyagun mutane da ke karamar hukumar Dawakin Tota a daren ranar Alhamis.
A cewar PPRO, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, sannan kuma ya amince da yin cinikin haramtattun kwayoyi.
“A ranar 4 ga Mayu, 2023 da misalin karfe 2200 na rana, an kama Ibrahim Musa, ‘m’ mai shekaru 22 a wani maboyar masu laifi a karamar hukumar Dawakin Tofa, jihar Kano bayan ya daba wa mahaifiyarsa mai shekaru 50 wuka har lahira a karamar hukumar Nassarawa, jihar Kano.
“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, sannan kuma ya amsa laifinsa na shan miyagun kwayoyi. Za a gurfanar da shi gaban kotu bayan an kammala bincike.”
BY ISYAKU.COM
Sai tinubu👍💪🙏🏼 Odaboo!
ReplyDeleteRUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI