Kotun ta kuma umurci ‘yan sandan Najeriya da su kammala bincike kan zargin cin zarafin wani dan sandan cikin sa’o’i 48 tare da barin Kuti ya koma gida. Saharareporters ta wallafa.
“Kotu ta ba ‘yan sanda sa’o’i 48 su kammala ‘binciken su’ daga nan za a iya barin Kuti ya koma gida a matsayin beli.
“Belin Kuti yana tare da sharadin mutum biyu da za su tsaya masa wadanda dole ne su kasance suna da kadarorin a Legas,” in ji wani ganau.
SaharaReporters ta samu cewa babban alkalin kotun ta kuma bukaci ‘yan sandan da su cire kansu daga gurfanar da shi gaban kuliya.
Ta kuma ba da umarnin cewa a kwafi fayil din karar a mika shi ga ofishin kula da kararrakin jama’a na jihar Legas domin gurfanar da shi gaban kuliya.
SaharaReporters ta ruwaito cewa masu gabatar da kara na ‘yan sandan sun yi ikirarin a kotun majistare cewa dan sandan da aka ci zarafinsa yana cikin suma, kuma yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Sai dai jawabin Lauyan Kuti ya nuna akasin haka, ya ce bayan aukuwan lamarin Dan sandan ya sami Kuti a gidansa ya bashi N12000 domin ya gyara motarsa.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI