Type Here to Get Search Results !

Tinubu Ya Gana Da Kwankwaso a Paris Kan Batun Shigowarsa Cikin Gwamnatinsa


Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu na APC ya yi wani zama da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP a birnin Paris da ke ƙasar Faransa.

Tattaunawar dai ta gudana ne a ranar Litinin da ta gabata, tsakanin Bola Tinubu da Kwankwaso, wacce ta ɗauke su tsawon sa'o'i hudu. Legit ya wallafa.

Tinubu ya ce yana shirin kafa “gwamnatin haɗin kan 'yan ƙasa” wacce za ta haɗa da ‘yan jam’iyyun adawa, dalilin Tinubu da rahotanni suka bayyana na zama da Kwankwason kenan.

Mutanen biyu sun kuma tattauna batun zaɓen shugabannin majalisar dokokin ƙasar da ke tafe. Jam’iyyar APC ta bayyana mutanen da ta ke so su jagoranci tagwayen majalisun.

Sai dai wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC na adawa da wannan tsari kuma sun yi barazanar sauya sheƙa zuwa jam’iyyar adawa idan har ba a sauya tsarin ba.

Jam'iyyar NNPP na da Sanatoci biyu da 'yan majalisar wakilai 19. Idan har waɗannan ‘ya’yan jam’iyyar za su haɗa ƙarfi da ƙarfe da ‘yan adawa, za su iya hana jam’iyyar APC samun rinjaye a yayin zaɓen.

Wadanda suka halarci ganawar baya ga Kwankwaso

Ganawar tsakanin Tinubu da Kwankwaso ta samu halartar Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa mai jiran gado.

Abdulmumin Jibrin, dan majalisar wakilai na NNPP kuma tsohon jigo a kungiyar yaƙin neman zaɓen Tinubu, shi ma ya samu halarta.

Oluremi Tinubu, uwargidan shugaban ƙasa, ta karbi Salamatu Kwankwaso, matar Rabiu Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu sun tuno da irin dangantakarsu da ta samo asali tun a shekarar 1992. A wancan lokacin Tinubu ya kasance Sanata ne, Kwankwaso kuma shi ne mataimakin kakakin majalisar wakilai.

Kwankwaso ya ce zai yi shawara da mutanensa

The Cable ta ce Kwankwaso ya ce zai tattauna da masu ruwa da tsaki a bangarorin biyu domin jin ta bakinsu kafin ya amince.

Ana sa ran Tinubu zai yi wa Kashim Shettima, da kungiyar gwamnonin APC, da sauran shugabannin jam’iyyar bayani, a yayin da shi ma Kwankwason zai yi haka ga shugabancin jam’iyyarsa.

Tinubu ya nuna damuwarsa kan alaƙar Kwankwaso da Ganduje

Tinubu ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano mai barin gado da Kwankwaso.

Ganduje ya kasance mataimaki ga Kwankwaso a lokacin yana gwamnan Kano daga 2011 zuwa 2015, kafin rabuwarsu.

Yanzu dai jama'a sun zura ido, suna jiran su ga ko Kwankwaso zai aminta da tayin shiga gwamnatin Tinubun ko a'a.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN