Dan Ta’adda Ya Yi Mutuwar Gaggawa Garin Fafatawa da DSS A Fitaccen Jihar Arewa


Wani wanda ake zargin dan ta'adda ne da yake dauke da kayayyakin fashewa a jikinsa ya mika kansa madakata saboda gudun kada a kama shi.

Lamarin ya faru ne a hanyar Ibrahim Haske a gundumar Keke dake cikin garin Kaduna a ranar Litinin 15 ga watan Mayu. Legit ya wallafa.

Shaidan gani da ido ya tabbatar da cewa an jiyo harbe-harben bindigogi da misalin karfe 1 na dare lokacin da jami’an farin kaya da sojoji da kuma ‘yan sanda suka zo kama wanda ake zargin.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lokacin da mutumin ya fahimci an yi wa inda yake kawanya, sai yayi amfani da wannan daman ya tada kayan fashewar

Artabu tsakaninsa da jami'an farin kaya da sojoji
Rahotanni sun tabbatar da cewa sunyi artabu sosai da jami’an tsaron kafin daga karshe ya kai ziyara barzahu.

Wata majiya ta jami’an tsaro ta bayyana cewa an samu bindiga kirar AK-47 a cikin gidan da kuma wasu abubuwan fashewa wadda daga baya jami’an kunce bam suka lalata shi.

Wani mazaunin unguwan kuma wanda ya kasance shugaba a yankin, Mallam Sama’ila ya tabbatar da faruwan lamarin inda yace jami’an tsaro sun tare mashigar gidan mutumin.

Yadda aka gano inda mutumin yake
Ya kara da cewa zai iya yiyuwa jami’an tsaron sun yi amfani da na’ura ne wurin gano inda mutumin yake don su kama shi.

Bayan mutumin ya fahimci babu wata hanyar tsira sai yayi tunanin cewa ga garinku nan da abubuwan fashewa a cikin gidan.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammad Jalige bai amsa wayarsa ba kuma bai maida martanin sakon kar ta kwana da aka tura masa ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN