Yanzu-Yanzu: EFCC Na Binciken Gwamna Matawalle Na Zamfara Kan Badakalar N70bn


Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ce tana binciken gwamnan jihar Zamfara¸ Bello Matawalle bisa zargin sama da fadi har na N70bn.

Hukumar har ila yau ta ce tsohon ministan wuta Sale Mamman da aka kama ‘yan kwanakinnan kan zargin sama da fadin N22bn yana tsare har yanzu. Legit ta wallafa.

Shugaban hukumar Abdulrashid Bawa ne ya bayyana haka a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu inda ya ce kada ‘yan Najeriya su damu da maganan da gwamnan ya yi dangane da yadda hukumar ke aiwatar da ayyukanta, cewar rahotanni.

Gwamnan ya zargi Bawa kan yadda yake nuna wariya a binciken EFCC, ya kuma kalubalanci hukumar EFCC da ta binciki mukarraban gwamnatin shugaba Buhari ba gwamnoni kadai ba, jaridar Daily Trust ta tattaro.

Bawa ya maida martani

Bawa wanda ya yi magana ta bakin daraktan kula da harkokin jama’a na EFCC, Osita Nwajah ya ce hukumar bai kamata ta mutunta gwamnan da martani ba, kawai ta yi ne don fayyace komai.

A cewarsa:

“Abin burgewa ne yadda Matawalle ke son zama shugaba wanda zai fada wa EFCC wanda za ta bincika. A wannan hali ‘barawo’ ne zai ce kada a taba shi sai an kama sauran ‘barayi’?

“Abin takaici ne yadda Matawalle zai bai wa EFCC umarnin wanda za su kama, wadanda ake zargi da suke hannun hukumar mu sun fito daga kowane bangare na al’umma.”
Waye EFCC ke kamawa?
Ya kara da cewa:

“Samun cancantar shiga komar hukumar shi ne idan ka aikata laifi, ba ruwanmu ko kai Fasto ne ko Limami, gwamna ko minista.
“A yanzu haka, tsohon ministan wuta yana hannunmu kan badakalar N22bn, wannan bai jawo hankalin Matawalle ba.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN