Adadin wadanda suka mutu a harin da aka kai a ranar Talata a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato ya kai 85 yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bace a yankunan da lamarin ya shafa.
Shugaban kungiyar ci gaban Mwaghavul na kasa, Joseph Gwankat ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba bayan wani taron tsaro da aka gudanar a fadar sarkin gargajiya a garin Mangu. ChannelsTV ta rahotu.
Gwankat ya yi nuni da cewa wasu da ake zargin makiyaya ne suka kai wa wasu al’ummomi hari a lokaci guda, lamarin da ya kai ga kashe-kashe tare da kona gidaje da kuma lalata gonaki a yankunan da lamarin ya shafa.
Mata masu zanga-zangar sun yi wa fadar sarkin gargajiya kawanya inda aka gudanar da taron tsaro tare da shugabannin tsaro da hakimai da jami’an gwamnati karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Farfesa Sonni Tyoden domin tunkarar kalubalen tsaro a karamar hukumar.
Mishkcham Mwaghavul, John Putmang Hirse, tare da shugaban karamar hukumar da hakiman gundumomi daga al'ummomin sun yi kira da a tura karin sojoji ga al'ummomin don kare 'yan kasa.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI