A wata sanarwa da Chris Uyoh, sakataren NLC ta kasa ya fitar, kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da matakin da Lamidi ya dauka a kotun zaben shugaban kasa a ranar Laraba, 17 ga watan Mayu, inda ta bayyana hakan a matsayin abin kunya. Kungiyar ta bayyana cewa abin takaici ne yadda Apapa, ke bayyana wa kansa "wani matsayi mara kyau a matsayin shugaban jam'iyyar Labour."
Ufot ya ce jam'iyyar Labour wadda NLC ta kafa fiye da shekaru talatin da suka gabata, ta samar da mambobi na hukumomi ga NLC da Trade Union Congress (TUC).
Kungiyar ta NLC ta ce, matakin da Mista Lamidi Apapa da tawagarsa suka dauka na nuna shakku kan yadda wasu masu sha'awar siyasa a Najeriya suka ci gaba da yin hakan, wadanda fatansu shi ne mutuwar jam'iyyar Labour.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI