An kama wani da ake zargin barawo ne yana satar igiyoyin wayar wutar lantarki a na’urar taranfoma a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
A cewar wakilin jaridar News Flash na jihar Adamawa a Maiduguri, wanda ake zargin ya dade yana satar igiyoyi wayoyin lantarki kafin daga bisani a kama shi da sanyin safiyar Laraba, 17 ga Mayu, 2023.
Fusatattun mutanen da suka kama shi, suka daure shi da karfen na’urar taranfoma.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI