'Yan Bindiga Sun Mamayi Jami'an Tsaro Sun Buɗe Musu Wuta, An Rasa Rayuka


Tsagerun 'yan bindiga sun halaka jami'an yan sanda uku a garin Umunze, ƙaramar hukumar Orumba ta kudu a jihar Anambra.

The Cable ta rahoto cewa 'yan sandan sun gamu da ajalinsu ne ranar Alhamis, yayin da 'yan bindigan suka kai farmaki shingen bincike da ke kan titin Umunze-Ihite.

Bayanai sun nuna cewa 'yan bindiga sun dira shingen binciken ba zato ba tsammani, suka buɗe wa yan sandan da ke bakin aiki wuta, nan take suka kashe uku.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yankin ya zama tamkar kufai, masu shaguna sun rufe wurin sana'arsu saboda tsoron abinda ka iya zuwa ya dawo.

"Lamarin ya faru da safe, yan bindiga suka kashe yan sanda uku, kowane farar hula ya yi takansa saboda harsasai ne kawai suke cin kasuwa a nan," inji shi.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar Anambra, Tochuckwu Ikenga, ya tabbatar da kisan jami'an guda uku ranar Alhamis.

A ruwayar The Nation, Ikenga ya ce hare-haren yan bindiga da sauran yan ta'adda na ɗaya daga cikin abubuwan da dakarun yan sanda ke fuskanta yayin da suke kan aiki.

Ya ƙara da cewa irin waɗan nan hare-hare ba zasu sa jami'an yan sanda su ja da baya ba, inda ya ce tuni hukumar ta kaddamar da aikin farautan makasan domin kamo su.

A kalamansa, kakakin yan sandan ya ce:

"Tuni muka tura karin dakaru zuwa yankin kuma a yanzun sun baza koma ta ko ina suna farautar makasan. Haka nan mun fara sintirin haɗin guiwa ba kama hannun yaro a yankin."

Jami'an rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar kwato ma'aikatan NGO biyu cikin uku da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a jihar Borno, arewa maso gabas.

Tun da labarin garkuwa da ma'aikatan ya bayyana, mahukunta ba su ce komai har kawo yanzu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN