Madalla: Sojojin Najeriya sun yi wa yan ta'adda mummunan barna sun aika da dama barzahu, sun kwace makamai


Dakarun Operation ‘Udoka’ dake fafutukar fatattakar ‘yan ta’addan IPOB/ESN a Kudu maso Gabas sun kai samame maboyar ‘yan kungiyar da ke Ihiala tare da kame tarin makamai da harsasai da suka hada da Bindigan Pump Action guda 49, Bindigogin AK 47 guda 3, AK 4.  Mujallun albarushi 47, Bindigan Dane 6 da harsashe 75 na musamman na 7.62mm da harsashi 3,371 masu rai yayin da aka kama wani dan bindiga daya.

 Hakazalika, sojojin sun kai samame kan wasu da ake zargin ‘yan Biafra/East Security Network a sansanonin ‘yan ta’addan da ke karamar hukumar Nkanu ta Gabas da kuma 9th Mile a karamar hukumar Udi ta jihar Enugu.

 Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

 Ya ce, “An yi kazamin fada, kuma an kashe ‘yan ta’adda, yayin da aka kama wasu 7.  Sojojin sun lalata sansanoninsu tare da kwato kyamarori 2 na CCTV, babura 8, kurtun rediyon bofeng guda 2, hular dajin soja 1, wayoyin hannu 3, wani abu da ake zargin cannabis tabar wiwi ne, wuka 1, guduma 1 da gatari 1.

 "Sojoji sun kuma kashe 1 daga cikin dan Indigenous People of Biafra/East Security Network, da 'yan ta'addar tare da kama 8. An ceto farar hula da aka sace da kuma kama 'yan ta'adda' an mika su ga hukumar da ta dace don daukar mataki".

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN