Yadda Tinubu Ya Yi Amfani da Obi, Ya Hana Atiku Samun Mulki Inji ‘Dan Takaran LP


Ibadan, Oyo - Tawfiq Akinwale wanda ya yi wa jam’iyyar LP takarar Gwamna a jihar Oyo ya bayyana abin da ya faru a zaben 2023 ta bayan fage.

Da aka yi hira da shi a gidan rediyon YES FM a garin Ibadan, Tawfiq Akinwale ya ce Asiwaji Bola Tinubu ne ya roki Pat Utomi ya hakura da takara. Legit ya wallafa.

Zababben shugaban kasar ya shawo kan Farfesa Utomi, ya bar Peter Obi ya nemi kujerar shugaban kasa a madadinsa a jam’iyyar LP mai adawa.

Dan takaran Gwamnan yake cewa har Utomi ya samu takarar shugaban kasa, amma da Tinubu ya lallabe shi, sai ya kyale Obi ya rike tutar jam’iyyar.

Akinwale ya ce Tinubu ya kware sosai a siyasa, rokon Utomi da ya yi ya hakura da neman takara a 2023 ya jawo Peter Obi ya yi wa jam’iyyar PDP illa.

An hana Atiku kai labari

An rahoto jigon na LP ya na mai cewa zababben shugaban kasar ya yi haka ne saboda ya toshe damar da Atiku Abubakar yake da ita na yin nasara.

A jawabin da ya yi da Yarbanci a gidan rediyon, ‘dan siyasar ya bayyana tsohon Gwamnan na Anambra da yaron Tinubu, ya ce da shi APC tayi amfani.

Haka zalika ‘dan siyasar ya yi ikirarin cewa kudin da Tinubu ya ba Utomi ne aka yi amfani da su wajen tallata Obi wanda a karshe ya ba kowa mamaki.

Mista Akinwale ya ce Tinubu bai yi tunani ‘dan takaran na LP zai iya irin farin jinin da ya yi a zaben na bana ba, ya samu kuri'u fiye da miliyan shida.

Obi ya samu tikiti a sama

Bayan ‘dan takaran mataimakin shugaban kasan 2019 ya bar PDP ne Utomi, Faduri Joseph da Olubusola Emmanuel-Tella su ka janye masa takararsu.

‘Dan siyasar ya samu tutar LP ba tare da hamayya ba, a karshe ya hana jam’iyyar adawa ta PDP samun kuri’u a Kudu maso kudu da kudu maso gabas.

Zaben jihar Kano

Labari ya zo cewa a yau za a fara sauraron shari’ar Abdulsalam Abdulkarim Zaura da hukumar INEC, jam’iyyar NNPP da Rufai Hanga a kotun karar zabe.

NNPP ta samu kujerun Majalisar Dattawa biyu a 2023, ‘Dan takaran na APC watau AA Zaura ya na so ya karbe daya, a cewarsa magudi aka yi aka doke shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN