Wani mai suna Ibrahim Omo-Alijana ya nemi ya saki matarsa Kudirat Ibrahim a kotun yanki da ke Centre-Igboro, Ilorin bisa zargin taurin kai da matarsa ta yi.
Sai dai wadda ake kara ta shaida wa kotun cewa ba za ta iya barin aurenta ba bayan ‘ya’ya shida.
Ta roki kotu da ta roki mijinta kada ya sake ta.
Alkalin kotun, AbdulQadir Uma, ya ce kotun ba ta karfafa kashe aure kuma a koda yaushe tana ba da damar sasantawa.
Don haka Umar ya dage sauraren karar zuwa ranar 12 ga watan Yuli, domin samun rahoton sasantawa ko kuma ci gaba da sauraren karar.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI