Ɗaliban jami'ar Benson Idahosa, Benin, babban birnin jihar Edo, sun fantsama cikin harabar makaranta suna zanga-zangar nuna fushi ranar Talata. Legit ya wallafa.
Daily Trust ta rahoto cewa ɗaliban sun ɓarke da zanga-zanga ne sakamakon mutuwar abokin karatunsu a jami'ar mai suna, Bruno Chigozie Ezeonye.
Marigayi dalibin, wanda ke shekarar ƙarshe a Kwas ɗin 'Computer Science' ya yanke jiki ya faɗi yana tsaka da buga wasan kwallo a filin wasanni, daga bisani rai ya yi halinsa.
Wata majiya daga cikin ɗaliban ta ɗora laifi kan Likitocin jami'ar sakamakon rashin duba shi cikin hanzari yayin da aka gaggauta garzayawa da shi Asibiti don ceton rayuwarsa.
Majiyar ta ce:
"Lokacin da suka zo kansa suka buƙaci a gaggauta kai shi Asibitin Faith Mediplex da ke kan Titin zuwa filin jirgi, mai alaƙa da jami'ar, sai Direban motar Ujila ya ce babu mai a motar."
Sakamakon mutuwar ɗalibin ne, abokan karatunsa na jami'ar suka ɓarke da zanga-zanga, suka lalata muhimman wurare domin nuna fushinsu da halayyar jami'an lafiya.
Yayin haka ne ɗaliban suka lalata ɗan karamin Asibitin cikin makaranta da kuma ofishin jami'an tsaron jami'ar daga bisani shugaban jami'ar, Bishop FEB Idahosa, ya samu nasarar kwantar masu da hankali.
Yayin da aka tuntuɓe shi, shugaban sashin sadarwa da dabaru na jami'ar, Temi Esonamunjor, ya ce:
"Hukumar makaranta zata fitar da sanarwa a hukumance nan ba da jimawa ba."
BY isyaku.com