Yadda Ganduje Ya Tattara Kayan Gwamnati, Yana Saidawa Iyalinsa – Kwamitin Abba


Kwamitin da Abba Kabir Yusuf ya kafa domin karbar mulkin jihar Kano ya zargi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da saida kayan gwamnati.

Legit.ng Hausa ta fahimci shugaban kwamitin, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya jefi Gwamnati mai barin gado da wannan zargi ne a yammacin ranar Laraba.

Abdullahi Baffa Bichi ya jagoranci jama’a zuwa ofishin wata ma’aikata da su ke zargin Abdullahi Umar Ganduje ya saida ta ga yaronsa, Abba Ganduje.

Jagoran na jam’iyyar NNPP ya ce har zuwa jiya, ma’aikatan gwamnari su ke amfani da ofishin, sai kwatsam aka ji cewa an yi gwanjonsa ga ‘dan Gwamna

Dr. Bichi ya kamanta aikin gwamnatin APC da fasa-kauri, ya ce ana tattara kayan da ke ma’aikatar. Wasu hotuna da ke yawo a Facebook sun karfafa zargin.

Ma'aikata guda a N10m?

Daily Trust ta rahoto Bichi ya na fadawa Duniya cewa NNPP ta samu labari an saida daukacin ma’aikatar ne a kan farashin da bai kai Naira miliyan 10 ba.

Zuwa 29 ga watan Mayun 2023, shugaban kwamitin karbar mulkin ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta fara dawo da duk kadarorin da aka yi gaba da su.

Daga dukiyar gwamnati da aka sace zuwa wadanda aka karkatar ko aka lalata, NNPP ta sha alwashin za su bar hannun ‘yan daidaikun da suka amfana.

Kwamitin ya kuma gargadi ‘yan kwangila da su guji taimakawa a abin da ya kira aika-aika. Duk abin da yake faruwa, gwamnatin Kano ba tayi magana ba.

Abin da ya faru a jiya
Kabiru Dakata ya yi magana a kan lamarin a shafinsa na Facebook, ya ce:

“Dazu mu na sakatariyar kwamitin karbar mulki, sai aka kiramu cewar ga shi chan an ce ma'aikatan Kano State Public Procurement Bureau su tashi an sayar da gurin.

Ina aka taba yin haka? Nan da nan jagororin babban kwamitin su ka dira gurin. Da nan gurin, da ireirensa kowa ya siya ya sayi WOFI.
- Kabir Dakata

An nemi tuntubar Kwamishinan labarai domin jin gaskiyar lamarin, amma jaridar ba ta same shi ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN