Ta faru: Wani Likita ya taushe Ma'aikaciyar jinya da bata da lafiya ya yi mata fyade a asibiti


Wata Kotun Majistare da ke Ilorin, a ranar Laraba, 10 ga watan Mayu, ta bayar da umarnin a tsare daraktan lafiya na asibitin Ayodele, Ilorin, jihar Kwara, Dokta Ayodele Joseph, a gidan gyaran hali bisa zargin yi wa wata mara lafiya fyade.


 A cewar rahoton farko na ‘yan sanda (FIR), ana zargin Likitan ya yi wa majinyaciyar nasa fyade, wanda aka ce ma’aikaciyar jinya ce, wadda ke kwance a asibiti domin neman magani. LIB ya wallafa.


 Rahoton ’yan sandan ya ce wanda ake zargin ya yi wa mara lafiyar kutsen mutuncinta, kuma daga karshe ya yi lalata da ita ba tare da izininta ba.


 "Ma'aikaciyar jinya ta je asibiti don neman magani lokacin da likitan, wanda ya yi iÆ™irarin cewa yana da gogewar shekaru 27 a fannin likitanci, ya yi amfani da ita wajen jinya," in ji FIR.


 "Bincike a cikin lamarin, ya kai ga dawo da faifan bidiyon da ke dauke da lalata da wanda ake tuhuma ya aikata,  yayin da gwajin lafiya ya tabbatar da cewa an ci zarafin ma'aikaciyar da kuma fyade."


 Dan sanda mai shigar da kara, Gbenga Ayeni, ya shaida wa kotun girman laifin da kuma bukatar da ke kunshe cikin rahoton ‘yan sanda na neman a tsare Ayodele a gidan yari.


 A hukuncin da ta yanke, Alkalin Kotun Mai shari’a Jumoke Kamson ta amince da bukatar mai gabatar da kara kuma ta bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali.


 Daga baya alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga Mayu, 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN