Kotun Musulunci a Kano ta tasa keyar matasa 2 zuwa Kurkuku bayan sun ci kwalan Limamin unguwarsu a Masallaci


Kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a PRP Gama cikin jihar Kano ta garkame mutane biyu bisa zargin cin zarafin wani limamin masallaci a cikin unguwar. Legit ya wallafa.

Wandanda ake zargin, Ada Yahaya da Muslim Ibrahim sunyi kokarin dukan limamin ne mai suna Mallam Muhammada Auwal Tsamiya wanda shine ya ke jan sallah a masallacinsa da ke Hotoro a cikin kwaryar Kano.

Mutanen biyu wadanda ake zargin, an tusa keyarsu ne zuwa kotu wanda Nura Yusuf Ahmad ke jagoranta kuma ana zarginsu ne da laifuka 3 da suka hada da cin zarafi da nuna karfi da kuma hadin baki.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mutanen biyu sun shake wuyan rigar limamin kuma suka jawo shi waje saboda basa sonshi a matsayin limamin masallacin.

Sun musanta zargin da ake musu
Bayan karanto musu laifukansu, wadanda ake zargin, Ada da Muslim sun musanta aikata wannan mummunan laifin.

Alkalin kotun ya bada umarnin tsaresu a gidan gyaran hali kuma ya daga sauraron karar zuwa wani lokaci.

Rahotanni sun tabbatar da cewa matasan bayan sun musanta zargin da ake musu, ba su nuna wani damuwa ko dana sani ba game da abinda ya faru, tuni aka tisa keyarsu zuwa gidan gyaran hali zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN