Wata mata mai shekara 30 mai suna Oluwaseun Bolatito da ke zaune a Legas, ta haifi diya mace a ranar Asabar, 7 ga Mayu, 2023. Ta yi ikirarin cewa tana da ciki na tsawon shekaru shida da wasu watanni.
Oluwaseun ta yi wa yaron baftisma “Anuoluwa”, ma’ana rahamar Allah. Vanguard ta ruwaito.
Sai dai Oluwaseun, wadda ta ce an yi mata ba’a a unguwarsu, ta shiga nakuda ne a ranar Juma’a da daddare, kuma ta haifi ‘ya mace a ranar Asabar a Anu Olu Convalescent Maternity Home a unguwar Mafoluku a Oshodi.
An tattaro cewa a lokacin da labarin haihuwar jaririnta ya isa ga al’ummarta, sai jama’a suka garzaya asibiti domin ganewa idanunsu.
Duk da haka, wani kwararren Likita wanda baya son a ambaci sunansa, ya shaida wa Vanguard cewa yana iya zama lamarin fibroid.
Ma'aikatan kiwon lafiya sun ba da shawarar gwajin da ƙwararru don tabbatar da ainihin abin da ya faru.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI