Yanzu-Yanzu: "Ba Makawa Dole Na Zama Shugaban Kasa a Najeriya," Peter Obi


Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party a babban zaben 2022 da ya wuce, Peter Obi, ya ayyana cewa dole ne ya zama shugaban kasa a Najeriya. Legit Hausa ya wallafa.

Mista Obi, wanda ya zo na uku a zaɓen shugaban kasa, ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da littafinsa mai suna, "Peter Obi: Many voices, one Perspectives”, a Awka, babban birnin jihar Anambra ranar Jumu'a.

Daily Trust ta rahoto cewa an shirya taron kaddanar da littafin ne da nufin tara kuɗin ɗaukar nauyin ƙarar da ya shigar gaban Kotun zaɓe, yana kalubalantar nasarar Bola Tinubu.

A kalamansa, Peter Obi ya ce:

"Duk wanda ke tunanin zan sa kafa na bar ƙasa nan yana ɓata lokacinsa ne, ya zama dole na zama shugaban ƙasa a Najeriya, idan ba yau ba, nan gaba."

Karin bayani na nan tafe...

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Iska na wahalal da Mai kayan Kara piter obi

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN