Da duminsa: An kama matar da ta yi garkuwa da diyarta yar shekara 6 ta nemi kudin fansa N3m daga tsohon mijinta a Kano


Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Raham Sulaiman, bisa zarginta da yin garkuwa da ‘yarta ‘yar shekara 6 mai suna Hafsat Kabiru tare da neman kudin fansa N3m daga tsohon mijinta.

 Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da matar tare da wasu wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban, a hedikwatar ‘yan sanda da ke Bompai a ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, 2023.

 Matar dai ta kai diyarta ga wani dan uwanta dake unguwar Madobi domin ya ajiye mata, inda ta ce za ta yi tafiyar kwanaki.

 A cewar CP, ‘yan sandan sun samu rahoto daga mijin, Kabiru Shehu, cewa an yi garkuwa da ‘yarsa.

 “A ranar 08/05/2023, an samu rahoto daga wani Kabiru Shehu na Sharada Quarters, karamar hukumar Kano Municipal cewa matarsa ​​da ya saki, Rahma Sulaiman ‘f’ ‘yar shekara 25 ta shaida masa cewa ‘yarsa mai suna Hafsat Kabiru, ‘f.  'Yar shekara 6 ta bace, kuma wasu da ba a san ko su waye ba sun kira ta ta wayar salula suna neman kudin fansa Naira miliyan uku (N3,000,000:00k)," in ji shugaban 'yan sandan.

 “A binciken da aka yi, an ceto karamar yarinyar a karamar hukumar Madobi.  An kama matar da aka sake ta kuma ta amsa cewa ta shirya, inda ta kai diyarta wani maboya sannan ta bukaci a biya ta kudin fansa.  Ana ci gaba da bincike.”

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN