Sanata Uba Sani, zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna, ya sanar da naɗinsa na farko, kwanaki kaɗan kafin a rantsar da shi, inda ya bayyana Muhammad Lawal, a matsayin sakataren watsa labaransa.
A cewar rahoton Tribune, Uba Sani ya yi duba ne da ƙwarewar da Lawal ya ke da ita, a ɓangarori daban-daban.
A cikin wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu, zaɓaɓɓen gwamnan na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa naɗin Muhammad Lawal zai fara aiki ne daga ranar Talata, 23 ga watan Mayun 2023.
BY isyaku.com