DSS Ta Bankado Kulla-Kullan Da Wasu Ke Yi Gabannin Rantsar Da Shugaban Kasa Da Gwamnoni a Fadin Najeriya


Rundunar tsaro ba farin kaya wato DSS ta ce tana sane da shirye-shiryen da wasu bata gari ke yi na tarwatsa bikin rantar da shugaban kasa da gwamnoni a ranar 29 ga watan Mayu a fadin kasar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Dr Peter Afunanya, ya saki a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu.

Afunanya ya ce manufar ita ce kawo karan tsaye ga kokarin hukumomin tsaro wajen tabbatar da gudanar da bikin cikin zaman lafiya da haifar da tsoro da fargaba tsakanin al'umma, jaridar The Nation ta rahoto.

Rundunar ta shawarci yan Najeriya da su bi ka'idojin tsaro da aka gindaya da kyau yayin gudanar da bikin rantsarwar.

DSS ta gargadi yan Najeriya gabannin 29 ga watan Mayu

Kakakin rundunar ya kara da cewar ana gargadin wadanda ba a ba izini ba da su nisanci wuraren da aka kebe da wasu wurare na musamman a wajen taron, rahoton Punch.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Idan za a iya tunawa a ranar 18 ga watan Mayun 2023, babban sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin mika mulki na shugaban kasa (PTC) ya gudanar da taron manema labarai na duniya inda ya bayyana tsare-tsaren rantsar da shugaban kasa.

"Babban abun jan hankali cikin tsare-tsaren shine rantsar da shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a Abuja. A wannan rana ne za a kuma rantsar da sabbin gwamnoni a yawancin jihohin.

"Saboda haka, rundunar na sane da shirye-shiryen da wasu bata gari ke yi na tarwatsa shirin a yankunan kasar. Manufar shine dakile kokarin hukumomin tsaro na tabbatar da anyi bukukuwan cikin zaman lafiya da kuma haifar da fargaba da tsoro a tsakanin jama'a.

"Bisa ga haka, ana shawartan yan kasa, kafofin watsa labarai da kungiyoyin jama'a da su bi ka'idoji tsaro yayin bukukuwan. Ana kuma umurtansu da su guje ma labaran karya, kokawar karya, 

karkatattun rahoto da labarai wanda ka iya rura wutar rabuwar kai, tayar da hankali da kuma barkewar rikici kafin da bayan taron. Hakan ya kasance ne daboda irin wannan ayyuka babu abun da zai amfani jama'a face lalata hadin kan kasar ."

A halin da ake ciki, rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da kwantar da hankalinsu sannan su bi doka inda ta ce za ta ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da an yi bikin rantsarwar cikin nasara.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN