Dan Najeriya ya saya wa karensa motar Naira miliyan biyu


Masu iya magana sun ce kowa ya dade zai ga dadau, wani dan Najeriya mai suna Doktor Skidon ya shirya gagarumin bikin don murnar ranar haihuwar karensa tare da saya wa karen motar Naira miliyan biyu
.

An gudanar da gagarumin bikin wanda ya samu halartar abokai da masoya a gidansa. Jaridar Aminiya ta wallafa.

A wani bidiyo da aka sa a shafukan sada zumunta an ga Doktor Skidon da abokansa suna sanya suturar shat kafin su fara yi masa ruwan kudi.

An yanka kek a yayin bikin inda daga nan Doktor Skidon ya raba alawa tare da taimakon abokinsa.

A cikin bidiyon an ji Doktor Skidon yana bayyana karen da dansa don haka ne ya zabi sayen motar da sunan karen.

“Ina son karena kamar dana, kuma ina son bikin ranar haihuwarsa ya zama na musamman.

“Ya cancanci a kyautata masa, kuma ina son in nuna masa yadda nake kula da shi,” in ji Doktor Skidon.

Gagarumin bikin ya samu bayyana ra’ayoyi mabambanta a shafukan sadarwar zamani, inda wasu suka caccaki abin da Doktor Skidon ya yi, yayin da wasu suka yaba masa kan nuna wa karensa kauna.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN