A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu


Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, ya ce rantsar da zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai kara masa karfin gwiwar neman kwace mulkin kasar nan. Legit ya wallafa.

Daily Trust ta rawaito cewa Tinubu ,wanda ya lashe zaben da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, za a rantsar da shi a matsayin babban kwamanda kuma shugaban Tarayyar Najeriya na 16 a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

Tuni shirye-shiryen taron rantsarwar ke ci gaba da wakana, inda jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da aikinsu yadda ya kamata.

Shirin rantsar da Tinubu ya kankama
Manyan baki da suka hada da tawagar shugaban kasar Amurka Joe Biden, sun isa babban birnin tarayya Abua domin halartar bikin mai muhimmanci ga 'yan Najeriya da ma duniya baki daya.

Da yake amsa tambaya mai alaka da bikin rantsarwar a wani shafin Twitter, Obi ya ce ba zai ja da baya ba a yakin neman tabbatar da nasararsa a zaben da ya gudana a bana.

A cewarsa:

“Ban fara wannan gwagwarmayar a rana daya ba; Na san ba zai zama abu mai sauki ba. Bikin rantsarwar za ta ma kara min karfi ne.”

Peter Obi ya mika sako ga masoyansa
Channels Tv ta ruwaito cewa, da yake aika sako ga fusatattun mabiyansa da ke babatu da tofin Allah-tsine ga Tinubu a kafafen sada zumunta, Obi ya ce:

“Ina rokonku ku tsaya cikin taitayinku. Wannan batu ne da ya shafi canji wanda ke daukar lokaci."

Amurka ta turo wakilai zuwa bikin rantsar da Tinubu

A bangare guda, gwamnatin kasar Amurka ta turo wakilanta don halartar bikin rantsar da Bola Ahmad Tinubu na Najeriya.

Gobe Litinin ne za a rantsar da Bola Ahmad Tinubu a matsayin sabon shugaban kasan Najeriya na 16 a jere.

Ya zuwa yazu yanzu, masu ruwa da tsaki na ci gaba da shiri, kasar Amurka ma ba a barta a baya ba tunda ta aiko wakilai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN