Wani da ’yan bindiga suka kai hari gidansu da nufin yin garkuwa da mahaifinsa a Jihar Kano ya yi dambe da su, ya kwaci mahaifin nasa.
An kashe dan bindiga daya a lokacin da masu garkuwa da mutanen suka yi kutse a gidan magidancin da ke kauyen Yarimawa da ke Karamar Hukumar Tofa ta jihar ne da nufin sace shi da dansa. Jaridar Aminiya ta ruwaito.
Amma ’yan bindigar suka gamu da gamonsu, inda dan mutumin ya turje ya hana su tafiya da shi, lamarin ya fara dambe da su.
Dan mutumin yana cikin dambe da ’yan bindigar ne sauran suka yi yunkurin su harbe shi, amma suka yi kuskure, suka dirka wa abokinsu harbi, ya mutu nan take.
Da yake gabatar da su bayan an kamo su, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel, ya ce, “Magidancin ya tsare, amma a kokarin maharan na kama dansa, sun harbi wasu mutum biyu da suka kawo dauki a kafa.
“An kai wadanda aka harba din Babban Asibitin Tofa domin ba su kulawa kuma har an sallame su.”
Ya ce daga baya da aka gudanar da bincike aka kamo mutum hudu da suka yi yunkurin yin garkuwa da mutanen.
Wadana ake zargin sun shaida wa ’yan jarida a hedikwatar rundunar cewa wani na kusa da iyalan magidancin ne ya tura su su yi garkuwa da shi da dansa.
Daya daga cikinsu ya ce, “Mun je gidan yadda aka ba mu umarni, amma dan mutumin ya turje, a garin harbin sa ne muka dirka wa abokinmu harbi. Amma ni ban ban taba yi ba, wannan ne na farko, kuma na yi nadama.”
BY isyaku.com