Type Here to Get Search Results !

Main event

"Tinubu Ba Zai Wuce Wata 6 Zuwa 7 a Kan Kujerar Shugaban Ƙasa Ba," Babban Jigo Ya Faɗi Abinda Zai Faru


Mamban jam'iyyar PDP kuma kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar, Daniel Bwala, ya ce PDP zata karɓe mulki daga hannun zababben shugaban kasa, Bola Tinubu. Legit ta wallafa.

Mista Bwala ya bayyana cewa PDP zata kwace mulki hannun Bola Tinubu watanni shida bayan rantsarwa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Babbar jam'iyyar adawa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa sun kalubalanci matakin INEC na ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa.

A ƙarar da suka shigar gaban Kotun sauraron ƙarar zaben shugaban kasa sun jera INEC, Tinubu da jam'iyyar APC a matsayin waɗanda suke tuhuma na 1 da na 2 da na 3 bi da bi.

A ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu, Kotu zata ci gaba da sauraron ƙarar Atiku da PDP.

PDP ta gane kuskurenta, ta nemi afuwar yan Najeriya
Da yake zantawa da Arise TV kan karar, an nemi Daniel Bwala ya yi karin haske kan ikirarin jam'iyyar APC cewa a tarihi babu jam'iyyar da ta yi ƙaurin suna wajen maguɗin zaɓe kamar PDP.

A kalamansa ya ce:

"Tun da daɗewa a shekarun da suka gabata PDP ta aminta cewa ta tafka kura-kurai a zamanin mulkinta. Zan iya tuna cewa lokacin da Secondus ya zama shugaban jam'iyya ya ba da hakuri."

"Ya jagoranci kamfe a sassan Najeriya yana faɗa wa yan ƙasa cewa PDP ta gane kuskurenta su yi hakuri su yafe mata. Ƙa taba jin APC ta nemi yafiya?"

Yadda zamu kwace mulki bayan wata 6 - Bwala
Dangane da kwarin guiwarsa kan ƙarar da PDP ta kai gaban Kotu, Mista Bwala, ya ce Tinubu zai hau gadon mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023 amma watanni 6 ƙaɗai zai shafe.

A cewarsa bayan waɗan nan watanni, Kotu zata tsige shi daga kujerar shugaban ƙasa ta maye gurbinsa da Atiku na jam'iyyar PDP.

"Idan (Tinubu) ya karbi mulki ranar 29 ga watan Mayu, watanni 6 zuwa 7 zai kwashe kan madafun iko kafin a sauke shi, daga nan zamu zo mu karbi haƙƙinmu."

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies