Fada ya kaure tsakanin Shugabannin Jam'iyyar LP a gaban Peter Obi a Kotu


Fada ya kaure tsakanin jagororin bangarorin Jam’iyyar LP a yayin zaman Kotun Sauraron Karar Zaben Shuaban Kasa.

Rikicin ya faro bayan shugaban bangaren jam’iyyar, Lamidi Apapa da magoya bayansa suka hallara a harabar kotun da ke sauraron karar da jam’iyyar da dan takararta na zaben shugaban kasa, Peter Obi suka shigar na kalubalantar nasarar Bola Tinubu na APC. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Lamidi Apapa, wanda ke rikicin shugabanci da shugaban jam’iyyar da aka dakatar, Julius Abure, ya yi kokarin zama a inda jami’an jam’iyyar ta LP ke zaune, amma kan ka ce kwabo aka fara cacar baka.

Wani daga cikin jami’an jam’iyyar ya ce wa Lamidi, “Kai kuma daga ina?” inda shi kuma ya kada baki ya ce, “Ba ka san ko ni waye ba; to kai waye kai? Ji yadda kake magana.”

Ana cikin haka, Apapa ya daga murya, ya ce masa, “Tashi ka bar nan, nan ba wurin zaman irinka ba ne.”

Daga baya sakataren kotun, Josephine Ekperobe, ta shiga tsakani ta kwantar da kurar.

Daga bisani da kotun ta kira shari’ar jam’iyyar ta LP, Peter Obi da Jagorar Mata ta jam’iyyar, Dudu Manoga, suka gabatar da kansu.

Amma Apapa ya mike zai gabatar da kansa, a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, amma alkalin da kotun, Mai Shari’a Haruna Tsammani, ya dakatar da shi.

Ganin haka, sai Abure, wanda ke zaune kusa da Peter Obi, ya ki mikewa ya gabatar da kansa.

A baya dai Lamidi Apapa ya lashi takobin janye karar da ke gaban kotun, bayan da Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Abure.

Amma dai jam’iyyar ta daukaka kara.

A zaman nan ranar Laraba lauyan LP da na Bola Tinubu da na APC da na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za su gabatar da bayanin yadda suka hade batutuwan da kotun za ta yi shari’a a kansu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN