Wani matashi dan shekara 24 mai suna Musa Abdullahi dan unguwar Riga Fada da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano ya gurfana a gaban wata kotun majistare bisa zarginsa da kona gidan su tsohuwar budurwar sa wadda ta jefar da shi ta koma ga wani mai neman aure.
Abdullahi wanda ake tuhuma da laifin yin barazana ga zaman lafiya da yunkurin aikata kisan kai, an kuma zarge shi da cinna wuta a gidan iyayen tsohuwar budurwar tasa wanda ya kai ga kone wasu sassan jikinta.
Lauya mai shigar da kara, Barista Amal Bashir Albasu, ta roki kotu da ta karanta wa wanda ake kara tuhumar.
Bayan sauraron tuhume-tuhumen, Abdullahi ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, inda Alkalin kotun, Rabi Abdulkadir ta ce a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Yuni.
BY isyaku.com