Majalisar Dokokin Najeriya Ta Amince Da Dokar Ba ‘Yan Kasa Damar Tsayawa Takara Ba Tare Da Jam'iyya Ba


Kuma tuni an mika dokar ga shugaban kasa domin ya rattaba mata hannu ta zama doka. Daga dukan alamu dokar ta samu karbuwa domin ‘yan majalisar sun ce dokar ba ta su ba ce.

ABUJA, NIGERIA - Wannan doka da majalisa ta gabatar ita ce dokar sauya kundin tsarin mulki mai lamba 58, wacce a yanzu haka ta samu amincewar Jihohi 31 daga cikin jihohi 36 na kasar, wanda ya nuna cewa an samu kashi biyu bisa uku na yawan jihohin da ake so su amince da kudurin dokar kafin ya zama doka.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa Ibrahim Abdullahi Gobir ya yi karin haske cewa wannan doka za ta yi tasiri sosai a kasar domin za a kai faggen da wanda duk mutane ke so shi za su zaba. Saboda haka ba dole bane sai mutum ya tsaya a karkashin Jamiyya, domin ya nuna cewa an ba ‘yan siyasa ‘yanci kuma don haka yana da kyau sosai.

Gobir ya ce ba wai 'yan Majalisa ne suka kawo dokar ba, ‘yan kasa suka kawo dokar kuma Majalisa ta yi aikin ta. Gobir ya ce dokar tana cikin dokokin 44 da Majalisar kasa ta riga ta yi gyara akan su, kuma an samu amincewar kashi biyu bisa uku na jihohin kasar 36, saboda haka an aika wa shugaban kasa dokar domin ya sa mata hannu.

Shi ma mataimakin mai tsawatar wa a Majalisar Dattawa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya kara jadadda hujjar amincewa da dokar da sharudan da dokar ta kunsa.

Sabi ya ce ba haka kawai dokar ta zo ba, an lura cewa idan ba a sa sharuda ba, mutane za su fito da yawa, su ruda tsarin, tare da yi masa karan tsaye. Sabi ya ce sai mutum ya samu yawan adadin wadanda za su sa masa hannu a lokacin tsayawar sa takara, wanda shi ne zai taimakawa hukumar zabe wajen yin aikin ta na tantancewa.

A lokacin da yake nazari akan wannan batu na samun dokar da ‘dan siyasa zai iya tsayawa takara, kwararre a fannin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja Dr. Abu Hamisu ya ce abin murna ne samun wanan doka ganin cewa tuni kasashen da suka ci gaba suna aiwatar da ita.

Abu ya ce a nan Najeriya, dokar za ta ba da dama a samu mutane wadanda suke son sauye-sauye a yanayin mulki. Abu ya ce zai rage yawan koran mutane a jam’iyyu barkatai babu adadi saboda kawai mutum ya bayyana ra'ayin sa.

Kudirin ya tanadi cewa duk wani ‘dan Najeriya da ya ke so ya tsaya takarar shugaban kasa a matsayin ‘dan takara mai zaman kansa, dole ne ya samu sa hannun da aka tantance na akalla kashi 20 cikin 100 na masu kada kuri’a daga kowace jiha ta tarayya. Haka ya ke a takarar gwamna a jihar sa, da na ‘yan majalisu da ma shugabanin kananan hukumomi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN