Da Ɗumi-Dumi: Jami'an Tsaro Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar Arewa, Sun Hana 'Yan Majalisa Shiga


Jaridar Punch ta rahoto cewa an sake shiga yanayin tashin hankali da ɗar-ɗar a zauren majalisar dookin jihar Filato, Arewa ta Tsakiya, da safiyar Laraba.

Hakan ya biyon bayan ganin dakarun rundunar 'yan sanda reshen jihar sun mamaye zauren majalisar kuma sun kwace iko sun hana mambobi shiga. Legit ya wallafa.

Mamban majalisar dokokin jihar, Honorabul Gwottson, mai wakiltar mazaɓar Jos ta kudu ne ya tabbatar da faruwar haka ga jaridar a Jos, babban birnin jihar Filato.

Gwottson, wanda ya yi allah wadai da matakin dakarun 'yan sandan, ya ce lamarin ya hana mambobin majalisa taruwa domin ci gaba zama kamar yadda suka tsara yau Laraba.

Yayin da yake kokawa kan wannan yanayi da suka tsinci kansu a majalisa, ɗan majalisar ya ce:

"Mun yi zama jiya (Talata) ba tare da wata matsala ba kuma mun duba wasu muhimman kudirori, muka amince da wasu domin walwalar al'umma."

"Mun tsara zamu dawo yau (Laraba) mu ƙara zama domin ci gaba da ayyukan mu na ɓangaren masu doka, ba zato jami'an 'yan sanda suka mamaye zauren."

"A matsayin na yan majalisa bamu san wani dalili da yasa yan sanda suka sake kwace zauren majalisa a karo na biyu ba, suka hana mambobi sauke nauyin da ke kansu."

Mista Gwottson ya ƙara da cewa zasu kira taron menama labarai nan ba da jimawa ba domin jawo hankalin duniya kan abinda ke faruwa a jihar Filato saboda yan sanda na kokarin kashe demokuraɗiyya.

Idan baku manta ba, jami'an yan sanda sun kwace zauren majalisar dokokin Filato watanni biyu da suka shiga har suka garkame zauren da kwado, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Tin wancen lokacin mambobin majalisar ba su samu ikon zama ba sai jiya Talata 30 ga watan Mayu, 2023, awanni 24 bayan rantsar da sabon gwamna, Caleb Mutfwang.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN