Tap di Jan: Gwamnan APC Ya Nada Sabon Kwamishina Yana Dab Da Sauka Kan Mulki


Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi sabon naɗin kwamishina yana dab da yin bankwana da kujerar mulkin jihar Kano.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa, gwamna Ganduje a ranar Juma'a ya rantsar da sabon kwamishinan hukumar zaɓe ta jihar. Legit ya wallafa.

Rantsar da sabon kwamishinan na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya bayan gwamnan ya umurci dukkanin masu riƙe da mukaman siyasa a jihar, da su ajiye muƙamansu zuwa ranar Juma’a.

Abdullahi Abba Sumaila, ya zama sabon kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), bayan ya yi rantsuwar kama aiki.

Rantsuwar kama aikin sabon kwamishinan ta gudana ne a zaman majalisar zartaswar jihar na ƙarshe a daren ranar Juma'a, 26 ga watan Mayun 2023.

Ganduje ya buƙace shi da ya yi aiki tuƙuru
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje lokacin da yake jawabi bayan rantsar da sabon kwamishinan, ya ce an ba kwamishinan rantsuwar kama aiki ne bayan majalisar dokokin jihar Kano ta tantance shi.

Ganduje ya ce bayan tantancewar da majalisar ta yi masa, ta kuma amince da aka naɗa shi muƙamin kwamishina.

Gwamnan ya buƙace shi da ya yi aiki yadda ya dace saboda girman muhimmancin da hukumar ta ke da shi a jihar Kano.

A kalamansa:

"Muna fatan cewa zaka gudanar da aikin ka yadda ya dace saboda muhimmancin da kujerar da aka baka ta ke da ita, musamman wajen gudanar da zabukan ƙananan hukumomi a jihar Kano."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN