Lale marhabin da "First Lady" sabuwar matar Shugaban kasar Najeriya Oluremi Ahmed Bola Tinubu


Oluremi Ahmed Bola Tinubu ita ce sabuwar "First Lady" watau mmatar Shugaban kasar Najeriya da za ta karbi martabar matsayin saga Aisha Buhari. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.

Duk da yake babu tsari na tafiyar da ofishin matar Shugaban kasa a Najeriya a cikin kundin tsarin  mulki. Sai dai babu yadda za a iya kawar da kai duba da irin muhimmanci da ke tattare da ofishin a.mahanga ta siyasa, zamantakewar, tattalin arziki da tsaro.

Daily Trust ta ruwaito a ranar Asabar din da ta gabata cewa, a cikin takardar Tinubu/Stettima mai suna “Action Plan for Better Nigeria”, gwamnati mai zuwa ta gabatar da tsare-tsare na ci gaban mata, wadanda suka hada da hada kan al’umma da karfafa siyasa, karfafa tattalin arziki, yaki da cin zarafin Mata, da cin zarafi a cikin gida da kuma  a matsayin cimma Ilimin zamani.

 A cikin takardar, gwamnati mai jiran gado ta yi alkawarin ba mata kashi 35 cikin 100 na dukkan mukaman gwamnati.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN