Jerin Manyan Matsaloli 5 da Ke Jiran Tinubu da Zarar Ya Karbi Buhari


Bola Tinubu, zababben shugaban kasa zai karbi mulki daga hannun Buhari a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu, zai zama sabon jagoran kasa.

Najeriya dai kasa ce da kowa ke cikin dimuwa, kasa ce da ke fuskantar kalubale daban-daban, kuma mutane sun kagu don ganin Tinubu ya kawo sauyi na gari. Legit ya wallafa.

Kashim Shettima, mataimakin Tinubu ya amince da matsalolin da kasar ke ciki a ranar 26 ga watan Mayu, inda ya bukaci mutane da su sanya gwamnatin nasu a addu’ar nasara.

Kadan daga abin da ke jiran Tinubu akwai:

Batun tallafin man fetur
Tallafin man fetur na daya daga cikin abubuwan da ke kara jefa Najeriya cikin fatara da kuma lamushe kudaden kasar.

Masana tattalin arziki a lokuta da dama sun sha ba da shawarin a gaggauta cire tallafin man fetur don dawo da kasar kan turbar ci gaba da habakar kudaden shiga.

Gwamnatin Buhari ta yi alkawarin cire tallafin mai, amma ta gaza daga baya tare da kakaba wa Tinubu wannan aiki a gwamnatinsa mai jiran gado.

Mabambantan farashin musayar Naira zuwa Dala
Wata matsalar, ita ce yadda Najeriya ke fama da rashin tabbas wajen musayar kudaden waje, musamman dalar Amurka, wanda hakan ya shafi tattalin arzikin kasar.

A lokuta da dama, Najeriya na yawan fama da matsalar musayar kudaden waje a kasuwanin bayan fage.

Wannan matsala ta jawo tsaiko ya tsayuwar daraja da farashin Naira a kasuwannin duniya, wanda kuma ya shafi tattalin arzikin kasar.

ASUU
Ba a gama da kitimurmurar kungiyar malaman jami’a ta ASUU ba, ga shi za a rantsar da Tinubu a ranar Litinin mai zuwa.

Kungiyar ta sha yin walagigi da karatun jami’a a Najeriya, inda ta zama kan gaba wurin yaji tare da zaman kus-kus da gwamnatin Buhari a lokuta mabambanta.

Har yanzu, ba a warware wasu matsalolin ASUU ba, don haka Tinubu zai ci gaba daga inda Buhari ya tsaya a gwagwarmayar gwamnati da masu ilimi a kasar.

NARD
Kamar dai ASUU, bata sauya zane ba ga kungiyar likitocin Najeriya ta NARD, wacce a kwanan nan ta janye yajin aikin kwanaki biyar na gargadi ga gwamnatin Buhari.

Wannan dai kamar tsallara haske ne ga tafiyar Tinubu a cikin duhu, don kuwa alamu na nuna za a kai ruwa rana da likitocin.

Ba wai gwamnatin Buhari ta yi yarjejeniyar da ba za ta kai ga gaci ba da likitocin ba, ta kai ga tsayar da batun da ba zai yiwu ba a gwamnatin Tinubu.

Rashin tsaro
Wata matsalar mai girma; batun rashin tsaro da ya addabi kowane yanki na kasar nan tun farkon mulkin Buhari har zuwa yanzu.

Daga Arewa zuwa Kudu, babu inda ake zaman lafiya a Najeriya, kuma tabbas gwamnatin Tinubu za ta gaji wannar damuwa daga ranar Litinin.

A wani jawabi, Shettima ya bayyana yadda shugaban kasa Tinubu zai tafiyar da kasar nan, ba kan turbar shari'ar Muslunci ba kamar yadda wasu ke tsoro.

Fatanmu Allah ya warware dukkan matsalolin Najeriya, ya kuma daura kasar a turba ta gari, ci gaba, zaman lafiya da habakar tattalin arziki.

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN