Tap di: Ganduje ya yi martani ga Kwankwaso, ya ce babu mai rushe masarautun Kano


Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce, bai kirkiri karin masarautun Kano guda hudu a gwamnatinsa don a rushe su ba. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a bikin ranar ma’aikata a filin wasanni na Sani Abacha da ke Kano, inda yace Allah ba zai turo wanda zai wargaza su ba.

Gwamnatin jihar Kano a baya ta rarraba masarautun Kano zuwa gida biyar, inda daga baya Ganduje ya tsige Muhammadu Sanusi II daga karagar mulkin Kano.

A wani bidiyon da aka gani yana yawo a kafar sada zumunta, sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP ya ce sabon gwamnan jihar ne ke da ta cewa game da sayadda sarautar Kano ke gudana.

Ya kuma bayyana cewa, kirkirar masarautun guda hudu kari kan masarautar Kano daya ta baya alama ce mai nuna hadin kai, ci gaba da zaman lafiyar al'ummar Kano.

“Na tabbata, kowanne daga cikinku idan ya je hedkwatar wadannan masarautu za ka tabbata cewa babu shakka an kawo ci gaba ga wadannan wuraren.

“Saboda haka, muna tabbatar muku, wadannan masarautun an yi su ne domin ba da hadin kai, wadannan masarautun an yi su ne domin ci gaba, wadannan masarautun an yi su ne domin tarihi, wadannan masarautun an yi su ne domin daraja sarautar gargajiya, wadannan masarautun an yi su ne domin daraja wadannan mutanen da ke zaune a wadannan wuraren.

“Kuma ina tabbatar muku, wadanann masarautun, dindindin sun zo da zama da gindinsu. Idan Allah ya yarda sai Mahdi ka ture, kuma Mahdin da zai ture Allah ba zai kawo shi ba.

“Kuma ina tabbatar muku ko ba ma gwamnati, muna nan muna addu’a Allah ya zaunar da wadannan masarautun.”

A baya Kwankwaso ya yi ishara ga makomar masarautun kano guda biyar da aka karkasa a gwamnatin Ganduje.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN