Daga cikin mutanen da aka kashe har da ’yan sandan kwantar da tarzoma shida da fararen hula 36 a kauyen Dan Umaru da ke Karamar Hukumar Damko Wasagu a Masarautar Zuru a Jihar Kebbi. Jaridar Aminiya ta wallafa.
Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa an gudanar da jana’izar mutum 27, wasu mutane da dama kuma sun samu raunuka a harin.
Sun bayyana cewa maharan sun kuma sace mutane da daruruwan dabbobi a kauyukan da ke makwabtaka da su.
A Jihar Zamfara kuma an kashe wasu mutum uku a wani kauye da ke Karamar Hukumar Shinkafi.
Sai dai har zuwa lokacin da muka kammala rubuta wanann labarin, hukumomin ’yan sanda ba su fiar ta bayani kan lamarin ba.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI