Inna lillahi: An bizine Safeto Musa Isa cikin Yan sandan kwantar da tarzoma Mopol 6 da Yan bindiga suka kashe a Masarautar Zuru jihar Kebbi


Yan bindiga sun kashe Safeto Musa Isa na Yan sandan kwantar da tarzoma MPF a karamar hukumar Danko Wasagu da tsakar ranar Lahadi 30 ga watan Afrilu.

Fafeto Musa Isa na daya daga cikin yan sandan kwantar da tarzoma 6 da Yan bindigan suka kashe a wani artabu da ya gudana tsakaninsu a garin Dan Umaru a karamar hukumar Damko Wasagu.

Marigayi Safeto Musa Isa, suruki ne ga shugaban Kamfanin Seniora Int'l Ltd, kuma Mawallafin shafin labarai na yanar gizo na isyaku.com da ke gudanar da harkokinsa karkashin Kamfanin.

An binne Safeto Musa Isa a kauyen Dgoga da ke arewacin garin Kanya a kabarin gidansu kusa da kabarin mahaifiyarsa, kuma kusa da kabarin yayansa Marigayi Adamu bayan Sallar Isha'i ranar Lahadi 30 ga watan Afrilu 2023.

Yunkurin mu na jin ta bakin Kakakin hukumar Yan sandan jihar Kebbi SP Nafiu Abubakar ya ci tura, bayan kiraye-kiraye da sakon kar ta kwana na SMS da muka aika masa na neman bayanin Yan sanda dangane da lamarin, amma ba mu sami amsa ba kafin lokacin rubuta wannan labari.

Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com zai kawo maku cikakken bayanin Yan sanda kan lamarin da zarar rundunar ta saki bayaninta.

Shafin labarai na isyaku.com na isar da ta'aziyyarsa ga iyalai, Yan uwa da abokan arzikin Marigayi Musa Isa, da sauran hazikan Yan sandan da suka rasa rayukansu wajen kare al'ummar Masarautar Zuru. Allah ya jikansu ya yi masu rahama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN