Ta faru: Yaki ya barke gadan-gadan a Sudan, Fadar shugaban kasa, biranen Khartoum, Omdurman na shan luguden wuta

 

Tuni dai yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Sudan da ta fara aiki a ranar alhamis ta lalace, inda aka kai hare-hare ta sama da kuma luguden wuta a kusa da fadar shugaban kasa da ke babban birnin kasar Khartoum da safe, a cewar Al-Jazeera.

 An kuma ji karar harbe-harbe a garin Omdurman da ke makwabtaka da shi, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana a shafin Twitter. Daily trust ta rahoto.

 Yarjejeniyar tsagaita bude wuta na mako guda da bangarorin biyu a rikicin Sudan suka amince da ita, ya kamata ta fara aiki daga ranar Alhamis har zuwa ranar 11 ga watan Mayu. Sai dai ana ganin damar da za ta iya samu ta yi kadan.

 Tun lokacin da aka fara fada a Sudan tsakanin bangarorin soji masu biyayya ga manyan janar-janar biyu kusan makonni uku da suka gabata, an sha yin shawarwarin tsagaita bude wuta na tsawon sa'o'i 72, sai dai an sha karyawa.

 Shugaban kasar Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ne ke jagorantar sojoji a fafatawa da tsohon mataimakinsa, Mohammed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar rundunar Rapid Support Forces (RSF).

 Janar-janar biyu sun taba kwace iko a Sudan tare a wani juyin mulkin hadin gwiwa da sojoji suka yi.

 Sai dai kuma rashin jituwar da aka yi ta yi kan yadda za a raba madafun iko ya haifar da sabani a tsakanin sansanonin biyu, wanda ya kai ga fada a tsakanin bangarorin a ranar 15 ga Afrilu, ya kuma jefa kasar da mazaunanta kusan miliyan 46 cikin wani mummunan rikici.  (dpa/NAN)

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN