Kuwa bayan yaki: Gwamnati ta raba wa wadanda aka kwaso daga Sudan N100k, katin N25k da data 1.5GB


Gwamntin tarayyar Najeriya ta karbi rukunin farko na ‘yan Najeriyan sama da 350 da suka makale a Sudan kana suka tsere Masar a ranar Laraba 3 ga watan Mayu.

A lokacin da suka sauka, gwamnatin tarayya ta raba musu kudi N100,000 kowannensu tare da kara musu N25,000 na katin waya da kuma 1.5GB na data. Legit ya wallafa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an yi rabon kudin ne a karkashin ma’aikatar jin kai. Minista Sadiya Umar Farouk ce ta tabbatar da hakan a yau Alhamis 4 Mayu, 2023 a filin filin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ta kuma tabbatar da cewa, dukkan mutum 350 da aka kwaso sun sauka a Abuja da misalin karfe 11:35 na dare, inda gwamnatin tace ana ci gaba da kokarin kwaso wasu.

Da take bayanin yadda aka raba tallafin da kuma wadanda suka ba da kudi da katin, ministar ta ce, kamar yadda NairaMetrics ta ruwaito.

“Ina godiya ga dukkan al’ummar da suka yi kokari wajen tabbatar da wadannan mutanen sun dawo lafiya kuma a mutunce. Muna godiya ga kamfanonin sufurin bisa tallafinsu.

“Akwai kudi N100,000 da zai kai su ga ahalinsu wanda tallafi ne daga gidauniyar Dangote ta hanyar ba su kudin sufuri da kuma katin waya na 25,000 daga MTN da kuma 1.5GB data daga MTN.

“Duk wani kokari an yi shi kuma kowa ya ba da gudunmawa wajen tabbatar da akalla wadannan ‘yan Najeriyan sun samu hanyar dawowa gida lafiya.”

A cewar ma’aikatar, za a kashe $1.2m wajen hayar motoci bas da za su yi jigilar ‘yan kasar gabanin kwaso su zuwa Najeriya kai tsaye.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN